Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Bayt (AS) – ABNA – ya ruwaito cewa: Sojin ruwan Rundunar Kare Juyin Juya Hali a Iran, a yau Alhamis, sun bayyana kwace wani jirgi maras matuƙi na bincike da yaudara na Amurka, a yammacin mashigar Hormuz, da saukar da shi a ƙasa lafiya.
Sun bayyana cewa mayaƙansu sun yi nasarar saukar da jirgin leƙen asiri da yaudara, nau'in "MQM-170," lafiya, suna mai nuni da cewa aikin sa shi ne lura da tsare-tsaren kariyar sararin sama na Iran a bakin tekun Farisa da mashigar Hormuz.
Fashewar Jiragen Dakon Mai 3 A Hanya Maras Izini A Hormuz
A bangare jiragen dakon mai, sojin ruwa na Rundunar sun bayyana cewa jiragen da suka keta doka 3 sun fuskanci fashewa da konewa cikin sa'o'i 24 da suka gabata, kuma an bar su a gabar kudancin mashigar, saboda wucewarsu ta hanyar da ba a ba da izini ba a mashigar.
Kira Da Kada A Kula Da "Mafarkin CENTCOM" Da Nanata Tunkarar Duk Wani Aiki Na Tunzura Da Ƙarfi
Sojin ruwa sun ƙara da cewa jiragen sun kashe dukkan tsare-tsaren radar da na’urorin da suke da su, kuma sun yi ƙoƙarin fita ta hanyar kudancin da ba a ba da izini ba, suna masu watsi da gargaɗin rundunar sojin ruwa ta Rundunar, kafin su fashe sakamakon ci karo da nakiyoyin ruwa.
Sun nanata cewa hanyar da ba a ba da izini ba "cike take da nakiyoyi," suna masu dora alhakin duk abinda ya sami jiragen da sukai gigitar bi ta wajen akan masu jiragen ruwa da ma'aikatansu ta waɗannan hanyoyin.
Haka kuma, sojin ruwa na Rundunar sun yi kira ga masu jiragen ruwa da ma'aikatansu da kada su kula da "mafarkin" hedkwatar rundunar Amurka "CENTCOM" a shafukan sada zumunta, suna mai nanata cewa "gaskiyar tana bayyana a fagen daga," suna mai tabbatar da cewa duk wani aiki na tunzura da ke watsi da ka'idojin da ke tafiyar da mashigar, tare da goyon bayan sojin Amurka da suka kwatanta da "ta'addanci da mamayewa," za a tunkare shi da ƙarfi.
Hedkwatar rundunar Amurka "CENTCOM" ta yi iƙirarin, a cikin wani rubutu a dandalin "X," cewa dukkan manyan hanyoyin wucewa "da aka amince da su a ƙasa da ƙasa" a mashigar Hormuz ba su da nakiyoyin ruwa bayan sojojin Amurka sun kawar da su, suna iƙirarin cewa dubban jiragen ruwa na kasuwanci sun yi amfani da waɗannan hanyoyin cikin aminci kuma suna ci gaba da wucewa ta cikinsu. Sun kuma ƙi rahotannin kan ci karon jiragen ruwa na kasuwanci da nakiyoyi yayin wucewarsu ta mashigar.
A wani sanarwa da ya zo daidai da sanarwar sojin ruwa na Rundunar kan konewar jiragen a mashigar Hormuz, hukumar ayyukan kasuwancin teku ta Biritaniya ta bayyana cewa kyaftin ɗin wani jirgi ya ba da rahoton ganin wani jirgi da ke cin wuta a nisan mil 9 arewacin birnin Khasab na Oman, ba tare da tantance dalilin gobarar ko asalin jirgin ba.
Iran tana nanata cewa wucewa ta mashigar Hormuz dole a yi shi tare da tuntubarta tana mai gargaɗi kan wucewa ta hanyar da ta sabawa doka da gujewa bin mafarkin Amurka a wannan fanni.
……………
Ra'ayinka